Rikici ya balle tsakanin gwamnoni akan Dino Melaye

Rikici ya balle tsakanin gwamnoni akan Dino Melaye

- Gwamna Emmanuel ya baiwa Dino lambar yabo

- Gwamnatin Kogi sunyi tir da wannan yabo

- Gwamnatin Kogi sun ce gwamnan yayi abin kunya

A ranar litinin din da ta gabata ne gwamnatin jihar Kogi ta kalubalanci gwamnan jihar Akwa Ibom Emmanuel Udom bisa ga wadansu kalamai da yayi akan sanata Dino Melaye saboda kokarin kiranyen da mazabar Dino suke yi.

A makon da ya gabata ne gwamna Emmanuel ya baiwa sanata Dino lambar yabo a wani taron kaddamarwa da gwamnan ya halarta. Gwamna yace Dino tamkar "Janar" ne a cikin sanatocin Najeriya kuma yana ganin kiranye bai kamace shi ba.

Gwamnatin Kogi tace Emmanuel ya bayyana irin kiyayyar da yake yiwa al'ummar mazabar Dino ne, don idan ba haka ba, ba zai saka bakin shi ba akan kiranyen da suke mishi ba kuma har yake yabon sanatan.

Rikici ya balle tsakanin gwamnoni akan Dino Melaye

Rikici ya balle tsakanin gwamnoni akan Dino Melaye

Rahoto daga babban kakakin gwamnan jihar Kogi yace, yunkurin da gwamna Emmanuel yayi na cewa Dino tamkar "Janar" ne a cikin sanatoci cin fuska ne akan sauran sanatocin, kuma ya dora Dino a matsayin da dayawa daga cikin sanatocin suka fi shi.

KU KARANTA: Zahra Buhari ta yi sharhi a kan halin da mahaifinta ke ciki

Yace tsananin kiyayyar mutanen yammacin Kogi ne inda sanatan ke wakilta yasa gwamnan yake yabawa Dino baya da kokarin kiranyen da suke mishi domin samun canjin me wakiltar su a majalisar dattawa.

Ya kara da cewa gwamna Emmanuel bai ji nauyin yin wannan yabo ga akan Dino ba, don yayi wannan yabo ne a taron bikin kaddamar da wasu aiyuka da Sanata Goodswill Akpabio ya kaddamar. Sanatan ya bada tirakta 4, injinan samar da wutar lantarki sama da guda 800, setin na na'ura me kwakwalwa guda 100, kekunan dinki da makamantansu.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel