Ibo ne zai zama shugaban kasa a zaben 2019

Ibo ne zai zama shugaban kasa a zaben 2019

Shugaban jam'iyan UPP chief Chekwas Okire, yace lallai fa da su yan kabilar Igbo za'a dama a zaben shekaran 2019 mai zuwa

Ya bayyana hakan ne a ganawarsa da 'yan jarida bayan fitawarsa daga cikin dakin taron da suka yi na jam'iyar a jihar anambra ranar asabar.

Ibo ne zai zama shugaban kasa a zaben 2019

Ibo ne zai zama shugaban kasa a zaben 2019

Ya ce "akwai mutane da dama da suka can-canci zama shugaban kasa a cikin al'ummar Ibo, kuma su gudanar da shugabanci da adalci, ga sanin ya kamata da kyautata wa al'umma da kuma cika alkawari, sannan za su cire kasar nan daga halin da ta shiga na karayar tattalin arziki.

KU KARANTA: Ba kaya ba kudi EFCC ta yi ram da wani a Kaduna.

Jam'iyar mulki mai ci ta APC ta kasa cia alkawarin da ta yiwa jama'a samo canji daga shugabancin PDP, a Yayin da take neman shugabanci kasar nan ido a rufe, wadda hakan yana rage mata yawan magoya baya sosai.

Okorie ya ce "An ci moriyar ganga an ya da korenta, an yi amfani da mu a lokacin da ake neman shugabanci, da aka yi nasara war, an yi amfani da siyasa aka mai da mu saniyar ware wajen raba mukamai". Wannan jam'iyar za ta fitar da dan yankin kudu maso arewacin kasar do takarar sugabancin kasar a zaben da za a yi a 2019.

KU KARANTA: wata mata ta rasa ranta a sakamakon rashin jirgi a Newzeland.

Okorie ya ce Mutane su daina firgita, ko jin tsoro a duk lokacin da suka ji an ambaci sunan Biyafara, abu ne mai kyau ga kowani dan kasa ya nemi kwato hakkin sa daga wurin wadanda suke wurin da ake cutar da su. Fafutukar neman 'yanci yanada kyau kwarai da gaske, kamar yadda masana shari'a ta duniya suka tabbatar da haka, bai kamata a rika cin zarafinsu ba.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel