Aisha Buhari ta bayyana macen da ta wallafa hotunan shugaba Buhari a yanar gizo

Aisha Buhari ta bayyana macen da ta wallafa hotunan shugaba Buhari a yanar gizo

- Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta aska haske a kan wasu hotunan da aka wallafa a yanar gizo a karshen makon nan

- Hajiya Aisha Buhari ta ce hotunan mallakar Aisha Alubankudi ne, amma ba na kwanan nan ba ne

- Aisha Alubankudi ita ne mace da ke tsakanin shugaba Buhari da kuma ministan ma'adanai na kasa a cikin hotunan

Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana wanda ta wallafa wasu hotunan mijinta a yanar gizo a karshen makon da ta gabata a Landan wanda ta jawo cece-kuce tsakanin jama’a.

Hajiya Aisha Buhari ta ce wata yar Najeriya mazaunar Birtaniya mai suna Aisha Alubankudi ita ta wallafa hotunan.

Aisha Buhari ta bayyana macen da ta wallafa hotunan shugaba Buhari a yanar gizo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Alubankudi da ministan ma'adanai, Kayode Fayemi

Uwargidan shugaban kasar tace ko da yake hotunan sun kasance na kwarai da kuma mallakar ta, amma ba hotunan kwanan nan ba ne.

KU KARANTA: Munafukan miji na za su gane kuren su idan ya dawo - inji Aisha Buhari

Hajiya Aisha Buhari ta bayyana hakan ne ga majiyar NAIJ.com a cikin wani taƙaitaccen ganawa ta hanyar kakakin ta, Sulaiman Haruna.

“Hotunan basu fito daga gare mu ba, mallakar Alubankudi ne kuma ta amsa bincike hukumomi a kan al’amarin" . A cewar Haruna.

NAIJ.com ta tattaro cewa Aisha Alubankudi ne mace wanda ta ke tsakanin shugaba Buhari da kuma ministan ma'adanai na kasa, Kayode Fayemi a cikin hotunan da ke zagayawa a yanar gizo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel