Osinbajo ya amince da Alkalai 19 na Kotun Masana'antu

Osinbajo ya amince da Alkalai 19 na Kotun Masana'antu

- Osinbajo ya amince da sabbin alkalan kotun masana'antu

- Alkalan an zabo su ne daga Jahohi 19

- Za a rantsar da su ranar Juma'a a Kotun Koli

Mukaddashin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya amince da mukaman alkalai 19 na Kotun Masana’antu.

Osinbajo ya amince da sunayen alkalan bayan tantancewa da shawarwarin da Majalisar Shari’a ta bayar.

Soji Oye, daraktan bayanai na majalisar shari’a, ya bayyana hakan ne a ranar Talata. Yace: "Sabbin alkalan da aka zaba daga Jahohi 19 ne na Kasa, za'a rantsar da su ranar Juma’a."

Osinbajo ya amince da Alkalai 19 na Kotun Masana'antu

Osinbajo ya amince da Alkalai 19 na Kotun Masana'antu

Ga sunayen sabbin alkalan da aka zaba; Namtari Mahmood Abba (Adamawa), Kado Sanusi (Katsina), Adeniyi Sinmisola Oluyinka (Ogun), Abiola Adunola Adewemimo (Osun), Damulak Kiyersohot Dashe (Plateau), Opeloye Ogunbowale (Lagos), Danjidda Salisu Hamisu (Kano), Essien Isaac Jeremiah (Akwa-Ibom), Elizabeth Ama Oji (Ebonyi).

KARANTA: Muddin Ali Modu ya karbi PDP na bar siyasa

Akwai karin, Mustapha Tijjani (Jigawa), Arowosegbe Olukayode Ojo (Ondo), Targema John Iorngee (Benue), Ogbuanya Nelson S. Chukwudi (Enugu), Bashir Zaynab Mohammed (Niger), Galadima Ibrahim Suleiman (Nasarawa), Bassi Paul Ahmed (Borno), Hamman Idi Polycarp (Taraba), Alkali Bashar Attahiru (Sokoto), da Nweneka Gerald Ikechi (Rivers).

Ciyaman na Majalisar Alkalai, Alkali Walter S. Onnoghen zai rantsar da su a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuli da misalin karfe 3 na yamma a Kotun Koli ta Kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel