Wani masanin littafin injila ya yi ikirarin cewa an kirkiri labarin Yesu Almasihu ne don a mulki talakawa

Wani masanin littafin injila ya yi ikirarin cewa an kirkiri labarin Yesu Almasihu ne don a mulki talakawa

- Joseph Atwill ya yi ikirarin cewa labarin Yesu Almasihu jabu ne

- Daular Roma ta kirkire shi don ta mulki talakawa ne, ya yi ikirari

Wani masanin littafin injila a kasar Amurka ya yi ikirarin cewa dukkan labarin Yesu Almasihu ya kasance kirkiraren labari.

Da yake rubutu a shafinsa na yanar gizo, Joseph Atwill ya yi ikirarin cewa daular Roma tayi amfani da labarin a matsayin jabu da aka shirya don mulkar talakawa.

Ya rubuta: “Ana iya kallon addinin Kirista a matsayin addini, amma zancen gaskiya an gina ta ne sannan kuma akayi amfani da ita a matsayin tsari na mulkar zuciya domin a samar da bayi da suka yarda da cewan Allah ne ke bautar da su.”

Wani masanin littafin injila ya yi ikirarin cewa an kirkiri labarin Yesu Almasihu ne don a mulki talakawa
Masanin littafin injila Joseph Atwill. Hoto: covertmessiah.com

A cewar Atwill daular Roma ne suka kirkiri labarin ne kawai domin su mulki mutane sannan su samar da Karin bayi.

Kalli Atwill a yayinda yake bayyana kudirin sa a cikin wannan bidiyo:

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel