Makon gobe za a fara shirin koro Dino Melaye daga Majalisa

Makon gobe za a fara shirin koro Dino Melaye daga Majalisa

– Sanata Dino Melaye na iya barin Majalisar Dattawa

– Hukumar INEC ta fitar da jadawalin tantance kiraye

– Duk da umarnin Kotu Hukumar ta tasa Sanatan a gaba

Hukumar zabe na kasa INEC ta fitar da ranakun da za ta dauka wajen tantance kuri’ar mutanen da ke yunkurin yi wa Sanata Dino Melaye na Jihar Kogi kiranye.

Makon gobe za a fara shirin koro Dino Melaye daga Majalisa

Za a koro Dino Melaye daga Majalisa?

Kwanaki INEC ta aikawa Sanata Melaye takarda shirin kiranye sai dai ya ruga Kotu domin dakatar da wannan yunkurin. Kotu Tarayyar dai ta nemi a tsaida maganar na wani dan lokaci amma Hkumar INEc tace ba ruwan ta.

KU KARANTA: Ndume zai maka Gwamatin Buhari

Makon gobe za a fara shirin koro Dino Melaye daga Majalisa

Kwanakin Melaye a Majalisa sun kusa zuwa karshe

Hukumar zabe na kasa INEC za ta fara tantance kuri’ar ne a Ranar 19 na wannan watan da karfe 8:00 na safe har zuwa karfe 2:00 na rana. Idan har an tabbatar cewa mutanen mazabar sun nemi a maido Sanatan gida to zai bar Majalisa.

Dino Melaye ya dai nemi ‘Yan uwan sa Sanatocin kasar su hana wannan yunkuri na yi masa kiranye. Haka kuma Jam’iyyar APC ta Jihar Kogi ta shiga Kotu domin hana ayi wa Sanatan na ta kiranye.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Irin kokarin Gwamnan Jihar Osun Aregbosola

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel