Bani da hannu cikin yunkurin tsige Osinbanjo - Bala Mohammed

Bani da hannu cikin yunkurin tsige Osinbanjo - Bala Mohammed

- Bala Mohammed ya musanta zargin da ake masa

- 'Ibada ce ta kai ni Kasar Saudiya'

- Bai halarci taron da 'yan siyasa suka yi a Saudiya ba

Tsohon Ministan Abuja, Bala Abdulkadir Mohammed yace babu sa hannun sa a yunkurin tsige Mukaddashin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Bayan wani rahoto da ya aka yi na ganawar wasu ’yan siyasa a Kasar Saudiyya don yunkurin tsige Mukaddashin Shugaban Kasa.

Bani da hannu cikin yunkurin tsige Osinbanjo - Bala Muhammed

Bani da hannu cikin yunkurin tsige Osinbanjo - Bala Muhammed

Tsohon Ministan ya musanta hakan; Yace: "babu ni a taron da 'yan siyasa suka yi a Saudi Arabia, Ibada ce kawai ta kai ni zuwa kasa mai tsarki."

Ya kuma kara da cewa: "ba a gayyace ni wani taro makamancin haka ba, ko da ko ace an gudanar da taron. Kuma ko da ace an gayyace ni, ba dalilin da zai sa na halarci taron."

Ya bayanna zargin hakan a matsayin bata mishi suna ziryan a bangaren siyasar shi.

KU KARANTA KUMA: MAsanin Linjila ya ce littafin kagagge ne

Tsohon ministan yayi kira da ‘yan siyasa da su kau da banbance-banbance a tsakaninsu, su hada kansu da Mukaddashin shugaban kasar don ganin samun cigaba a Najeriya.

Sai dai in bama son gaskiya muna munafuntar kan mu, amma Osinbajo yana iya bakin kokarin sa ganin ya toshe duk wata matsala da ta afku a rashin Shugaban Kasa. Kuma ina da tabbacin Buhari zai yi alfahari da shi.

Yana kuma kara kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da addu’ar da sukewa Shugaban Kasa don ganin ya samu lafiya. Da kuma addu’a ga Osinbajo don samun hikimar cigaba da tafiyar da mulkin Kasar nan har zuwa dawowar shugaban Kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel