Kaji yadda Kaji da Zakaru 5000 suka bazama akan wata babbar hanya tare da janyo cikas ga motoci? Karanta

Kaji yadda Kaji da Zakaru 5000 suka bazama akan wata babbar hanya tare da janyo cikas ga motoci? Karanta

- Wasu kaji da yawansu ya haura 5000 sun mamaye titin kasar Austria

- Hakan ya faru ne kuwa bayan hadarin motar dake safarar kajin

Jami’an kwana kwana sun kai gauro sun kai mari yayin da suka dinga fafatawa da wasu kaji su 7500 da suka balle daga akurkinsu yayin da ake safarar su, akan titin Asten, dake kasar Austria.

Wannan lamari ya faru ne a daidai loakcin da motar dake safarar kajin tayi hadari, wanda yayi sanadiyyar ballewar kajin, inda dukkaninsu suka ranta ana kare sun tsere akan titin, wannan ne yayi sanadiyyar dakata da tafiyar ababen hawa akan titin.

KU KARANTA: Cakwakiya a cikin gidan PDP: Ali Modu ya sake samun rinjaye akan Makarfi

Shugaba jami’an kwana kwana, Martin Pree yace “A gaskiya mun sha fama wajen kama wadannan kaji, zaka yi mamakin yadda sama da kaji 5,000 suka bazama akan titi. Don haka muka kama su, domin samar da sauki ga motoci.

Kaji yadda Kaji da Zakaru 5000 suka bazama akan wata babbar hanya tare da janyo cikas ga motoci? Karanta

Kaji yayin da suka balle

“Zamu tabbatar mun kama dukkanin kajin, amma fa bamu san lokacin da za’a bude hanyar nan ba, domin kama kaji 500 ba karamin abu bane.”

Kaji yadda Kaji da Zakaru 5000 suka bazama akan wata babbar hanya tare da janyo cikas ga motoci? Karanta

Jami'in kwana kwana ya kama wata

Ga bidiyon nan kamar yadda NAIJ.com ta kawo muku:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sabuwar hanyar kama barayi:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel