Rikicin Taraba: Mun rasa mutane 250 da dabbobi 4000 - Inji Fulani

Rikicin Taraba: Mun rasa mutane 250 da dabbobi 4000 - Inji Fulani

-Mun rasa rayuka 250 da dabobi 4000 a harin da ake kai mana a tsibirin Mambila

-Mutane sama da 1000 sun rasa muhallinsu sanadiyar harin Mambila

-Muna kira da gwamnatin tarayya da tayi bincike a kan harin Mambila

Rikici tsakanin makiyaya da manoma abu ne da ya dade yana ci ma mahukutan Najeriya tuwo a kwarya. A kwanan baya rikici ya balle tsakanin Makiyaya (Fulani) da mazauna garin.

Mai Magana da yawun kungiyar Miyetti Allah Kautal Horre na jihar Taraba yayi ikirarin cewa sun rasa mata da yara sama da 250 da kuma dabobi wanda yawan su ya kai 4000 a harin da aka kai musu a tsibirin Mambilla.

Rikicin Taraba: Mun rasa mutane da dabobi - Inji Fulani
Rikicin Taraba: Mun rasa mutane da dabobi - Inji Fulani

A ganawar da yayi da manema labarai jiya a garin Abuja, shugaba da kuma sakatare na kungiyar, Alhaji Bello Bodoje da Alhassan Saleh sun ce baza su yarda da duk wani kwamitin bincike da za’a kafa a jihar Taraban ba.

KUMA KU KARANTA: Boko Haram na da alaka da mayakan Al-Qa'ida na kasar Mali

Shugabanin biyu sunyi kira da mambobin kungiyan da su kwantar da hankulan su kuma su ci gaba da bin doka domin za su bi duk hanyoyin da doka ta shimfida domin warware matsalar.

Ya ce “Alkalluma da muke dashi ya tabbatar cewa an kashe mata da yara sama da 250, har illa yau an kasha dabobi 4000 kuma mutane 10,000 sun rasa muhallinsu, a yanzu suna fakewa ne a garuruwan da ke makwabtaka da mu a kasar Kamaru.”

Daga karshe Saleh yayi kira da gwamnatin tarayya da ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa da zai gano abin da ya hadasa fitinar da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel