Wasu gagararrun ýan fashi da makami sun faɗa tarkon Ýansanda a jihar Benuwe (HOTUNA)

Wasu gagararrun ýan fashi da makami sun faɗa tarkon Ýansanda a jihar Benuwe (HOTUNA)

Yansandan jihar Benuwe sun samu nasarar kama wasu gagga gaggan yan fashi su uku tare da sauran masu aikata miyagun laifuka a jihar da suka kai mutane 10.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Kaakakin rundunar yansandan jihar, Moses Joel Yamu a lokacin dayake bayyana yadda aka kama yan fashin, ya ambaci sunan wani daga cikinsu, Mike Solomon wanda ya shahara wajen fashin mota.

KU KARANTA: Rundunar sojin ƙasa ta samar da motocin yaƙi da aka ƙera a gida Najeriya

Kaakakin yace an kama Solomon ne a garin Enugu inda yaje don siyar da motar daya sata kirar Toyota Highlander mai lamba GBG 44 AA, wanda yayi fashinta a jihar Benuwe.

Wasu gagararrun ýan fashi da makami sun faɗa tarkon Ýansanda a jihar Benuwe (HOTUNA)

Gagararrun ýan fashi da makami

Sa’annan Yamu yace an kama Joseph John da Innocent Ejembi sanye da kayan sarki irin na Soji a karamar hukumar Ohimini, inda yace sun dade suna addabar mutanen yankin da fashi.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito jami’an rundunar Yansandan sun kai wani samame ne a mafakar yan fashi da suka hada da Tito Gate Gsm Shop, inda suka kama: John Okpara, Sunday Okori, David Akogwu, Anthony Emmanuel, Chia Wuese, Ujor Paul, Abdullahi Garba, Lucky Onunze, Tyolumun Samuel da Japheth Akabe.

Daga karshe Yamu yace nan bada dadewa ba zasu gabatar da yan fashin gaban kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani hukunci ya dace da barayi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel