Shugaban kasa Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Olumba Olumba

Shugaban kasa Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Olumba Olumba

- Shugaban cocin Brotherhood of the Cross and Star, Olumba Olumba Obu, ya bukaci taron jama’ar sa da suyi ma shugaban kasa Buhari adduá

- Olumba Olumba ya ce shugaba Muhammadu Buhari ba zai mutu a kan kujerar mulki ba

- A halin yanzu, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, taa bad a tsokaci kan samun saukin shugaban kasar

Yayinda ýan Najeriya da dama ke zullumi kan lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo kasar daga hutun san a jinya, shugaban cocin Brotherhood of the Cross an Star, Olumba Olumba ya ce shugaban kasar zai dawo kasar nan ba da jimawa ba.

Olumba Olumba ya ji wannan sanarwan ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli, yayinda ya bukaci dukkan sashi na kungiyarsa a Najeriya da suyi ma shugaban kasar adduá, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce: “Shugaban kasar Najeriya, shugaban kasarmu, zai dawo kasar nan ba da jimawa ba, sannan kuma zai dawo cikin koshin lafiya. Muyi adduá, mu gode ma Allah kan samun lafiyar sa.”

Shugaban kasa Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Olumba Olumba

Shugaban kasa Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba inji Olumba Olumba

Wannan ba shine karo na farko da Olumba Olumba ke tsokaci a kan lafiyar Buhari ba.

KU KARANTA KUMA: An cigaba: An kirkiro wayar da ba ta aiki da batiri

NAIJ.com ta tuna cewa a watan Mayu, 2017 malamin cocin ya bayyana cewa Buhari ba zai mutu kan karagar mulki ba.

A halin yanzu, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, taa bad a tsokaci kan samun saukin shugaban kasar.

A ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, uwargidan shugaban kasar ta buga a shafin Facebook cewa Allah ya amsa adduóín ýan Najeriya game da lafiyar shugaban kasar ta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel