An ci mutuncin ýar Najeriya Musulma a Landan don ta sanya hijabi (HOTUNA)

An ci mutuncin ýar Najeriya Musulma a Landan don ta sanya hijabi (HOTUNA)

- Wata baturiya ta tofa ma bakar fata majina a fuska a Landan

- Wannan bakar fata, Musulma ce kuma yar Najeriya ce

Wani abu daya faru a birnin Landan mai kama da nuna wariyar launin fata tare da cin mutuncin bakaken fata ya janyo cece kuce a shafukan sadarwar zamani, musamman daga Musulmai.

Wannan lamari mai cin rai ya faru ne a lokacin da wata mata ta baturiya farar fata tayi ma wata mata bakar fata, Musulma, sanye da hijabinta tofin majina a fuskarta hakanan babu gaira babu dalili.

KU KARANTA: Wani gwamna a yankin jihohin Arewa ya koma Da’awa (HOTUNA)

Ita dai wannan Musulma sunan ta Wasi, kuma aikinta shine daukan hoto a birnin Landan, Wasi da kanta ta bada wanann labara a shafinta na Tuwita, inda tace tana cikin tafiy tare da abokinta Aamer Rahman a tsakiyar garin Landan, sai ga wannan mata ta tare ta ta tofa mata yawu a fuska.

An ci mutuncin ýar Najeriya Musulma a Landan don ta sanya hijabi (HOTUNA)

Wasi, ýar Najeriya Musulma

NAIJ.com ta ruwaito nan da nan abokin Wasi, Aamer ya watsa hotunan baturiyar a Facebook.

An ci mutuncin ýar Najeriya Musulma a Landan don ta sanya hijabi (HOTUNA)

Baturiyar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wani direban fasto a Najeriya ya musulunta. Kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel