Dalilin da yasa hadin kan Najeriya ke cikin rudani – Atiku Abubakar

Dalilin da yasa hadin kan Najeriya ke cikin rudani – Atiku Abubakar

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce a yanzu haka hadin kan Najeriya na fuskantar barazana

- Atiku ya bayyana marigayi Maitama Sule a matsayin wani jigo mai son hadin kai wanda zaá yi kewan rashin sa sosai

- Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar ya bayyana mutuwar Maitama Sule a matsayin abu mai taba zuciya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce hadin kan Najeriya ya kasance a cikin wani hali bayan kira ga sake fasalin alámuran kasar.

Atiku ya yi sanarwan ne a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, lokacin day a kai ziyarar taáziya ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan rasuwar Danmasanin Kano, Yusuf Maitama Sule, jaridar The Guardian ta rahoto.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce mutuwar Maitama Sule wani kalubale ne ga burin samun hadin kan Najeriya, wanda a yanzu ke fuskantar barazana.

Dalilin da yasa hadin kan Najeriya ke cikin rudani – Atiku Abubakar

Marigayi Alhaji Maitama Sule

Atiku ya bayyana marigayin a matsayin wani jigo mai son hadin kai wanda zaá yi rashin sa sosai a kasar.

KU KARANTA KUMA: An cigaba: An kirkiro wayar da ba ta aiki da batiriAn cigaba: An kirkiro wayar da ba ta aiki da batiri

Ya bayyana cewa tsohon maáikacin huldan ya kasance salihin mutun sannan kuma cikakken mai kishin kasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga hadin kai, inganci da kuma ci gaban Najeriya.

Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa mutuwar Maitama SUle ya bar babban gibi da zaiyi wuya a cike ta, idan akayi laákari da gaskiyar marigayin wanda ya bauta wa alúmma.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel