Boko Haram na da alaka da mayakan Al-Qa'ida na kasar Mali - Buratai

Boko Haram na da alaka da mayakan Al-Qa'ida na kasar Mali - Buratai

- An ci karin Boko Haram

- An kama mayakan Boko Haram a Mali da Senegal

- 'Yan ta'addar suna neman daukar sabbin mayaka ne a kasashen yankin

Janar mai baiwa 'yan-ta'adda kashi, Tukur Yusuf Buratai, ya ce an gano alakar 'yan jihadin AlQaeda da ke arewacin Mali, suna da alaka da Boko Haram a Najeriya.

Ya kuma ce an kama masu kokarin daukar yara suyi safarar su zuwa filin daga daga Senegal da Mali. A baya ma dai, an sha gano hanyoyi na iyakar Najeriya da mayakan kan shigo da makamai ta arewa a Najeriya.

Boko Haram na da alaka da mayakan Al-Qaida na kasar Mali - Buratai

Boko Haram na da alaka da mayakan Al-Qaida na kasar Mali - Buratai

Janar Buratai, yayi kira da kasashen yankin Sahel da su kara bude ido su baza komar su domin dakile ta'addanci a yankin, inda ya kira ta'addanci da babbar barazanar tsaro da a yanzu duniya ta ke fuskanta.

A shekarun baya dai, suma mayakan na arewacin Mali, sun kori gwamnati daga arewa inda suka kafa sabuwar kasar su mai aiki da shari'ar Islama, suka kuma tumbuke hubbaren shaihunnan malamai da sufaye, a matsayin wurare na yin shirka.

KU KARANTA KUMA: Buhari ne zai lashe zaben 2019

Kasar Faransa dai ita ta shiga yankin na Azawad na Mali ta fatattaki mayakan masu kiran kansu 'yan kawar da bidi'a.

Tukur Buratai, ya ce an ci karfin Boko Haram tun daga ganiyar karfinsu a 2014, inda suka kafa daular su ta Islama a garin Gwoza da Mubi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel