Ba ni ba siyasa muddin kotun koli ta mikawa Ali Sheriff PDP, inji Bode George

Ba ni ba siyasa muddin kotun koli ta mikawa Ali Sheriff PDP, inji Bode George

- Bode George dai tsohon dan jam'iyyar PDP wanda ya rike mukamai daban daban, a baya har kurkuku ya zauna kan batun satar kudaden gwamnati, sai dai tsohon shugaba Goodluck ya yi masa afuwa.

Tsohon Soja, Janar Bode George, wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban PDP sannan ya rike hukumar fito ta teku a Lagos, NPA, ya ce muddin kotun koli ta mika wa Ali Modu Sherif jam'iyyar PDP to lallai ya hakura da siyasa, inda yace PDPn ma rugujewa zata yi.

A cewarsa, 'fatan mu shine wadannan alkalai su yi adalci, amma idan ba haka ba, to lallai mu kam baza mu yi jam'iyyar PDP wadda ke hannun Ali Sheriff ba.

Ba ni ba siyasa muddin kotun koli ta mikawa Ali Sheriff PDP, inji Bode George

Ba ni ba siyasa muddin kotun koli ta mikawa Ali Sheriff PDP, inji Bode George

Jam'iyyar Adawa dai ta PDP tuni ta dade tana cikin rikicin shugabanci, inda kotuna daban daban kan mika wa bangarorin jam'iyyar shugabancin jam'iyyar, wanda hakan ya kaisu ga kotun koli.

KU KARANTA KUMA: Buhari ne zai lashe zaben 2019

Janar din ya kuma yi tsokaci kan zabukan kananan hukumomi da za'ayi a jihar Legas a makwanni masu zuwa, inda ya ce PDP zata hada kai da wasu jam'iyyu domin cin zabuka.

Ya kuma yi kira da a sake wa Najeriya sabon tsari kan tattalin arziki, domin baiwa jihohi karin karfi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel