Zaben 2019: Kungiyar dattawan Arewa ACF ta gwalashe magoya bayan Buhari

Zaben 2019: Kungiyar dattawan Arewa ACF ta gwalashe magoya bayan Buhari

- Dattawan arewa sun gwalashe magoya bayan Buhari

- Dattawan sunce ba zasu goyi bayan kowa ba a 2019

- Dattawan sunce su ba yan siyasa bane

Wata kungiya ta magoya bayan shugaba Buhari mar rajin sake zabar sai a zabe mai zuwa wadda kuma ke da suna Muhammadu Buhari Legacy Implementation Initiatives a jiya sun kwashi kunyar su a hannun dattawan arewa nan na Arewa Consultative Forum (ACF) a turance.

Mun samu labarin cewa kungiyar da ke goyon bayan Buhari a zaben na 2019 mai zuwa ta kai wa kungiyar dattawan arewa ACF ziyarar ban girma ne a sakatariyar su dake a garin Kaduna inda suka bukaci da su goya musu baya su ma.

Zaben 2019: Kungiyar dattawan Arewa ACF ta gwalashe magoya bayan Buhari

Zaben 2019: Kungiyar dattawan Arewa ACF ta gwalashe magoya bayan Buhari

NAIJ.com ta samu labarin cewa amma sai dattawan na Arewa suka gwalashe su inda suka ce su kungiyar su ba ta siyasa bace don haka ba zasu goyi bayan kowa ba.

Da yake maida jawabi mataimakin kungiyar dattawan na Arewa Sanata Abubakar Girei ya kuma shawarci masu goyon bayan Buhari din da su sassauta ra'ayin su na nacewa kan lallai dole sai Buhari ne kadai zai iya gyara Najeriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel