Ba zamu kuma iya goyon bayan Buhari a 2019 ba - ACF

Ba zamu kuma iya goyon bayan Buhari a 2019 ba - ACF

- Komawar shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu na iya samun tangarda yayinda kungiyar Arewa ta janye goyon bayanta a gare shi

- Shugaban kungiyar yace zasu ba sauran shugabannin arewa dake da raáyin tsayawa takara goyon bayan su

- Kungiyar ta ACF ta bayyana cewa ta goyi bayan Buhari a 2015 saboda ya kasance dan takara daga Arewa, amma cewa wannan zai chanja a 2019

Kungiyar nan ta Arewa mai suna Arewa Consultative Forum (ACF) ta kaddamar da cewa bata goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dantakarar shugabancin kasa a shekarar 2019.

Kungiyar ta ACF ta bata tabbatar da goyon bayanta ga Buhari a 2019 ba.

Kungiyar ta ýan arewa ta bayyana cewa 2019 ya sha bambam da 2015, lokacin da ta kaddamar da cikakken goyon bayanta ga shugaban kasar da jamíyyar All Progressives Congress (APC).

Bazamu kuma iya goyon bayan Buhari a 2019 ba - ACF

Kungiyar Arewa ta ce bazata kuma goyon bayan Buhari a 2019 ba

Shugaban kungiyar yace zasu ba sauran shugabannin arewa dake da raáyin tsayawa takara goyon bayan su.

KU KARANTA KUMA: An cigaba: An kirkiro wayar da ba ta aiki da batiri

Kungiyar na maida martini ne bayan wata kungiya mai biyayya ga Muhammadu Buhari ta tunkare ta domin nema wa shugaban kasar goyon baya a 2019.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Ado Mohammed, shugaban kungiyar ta Muhammadu Buhari Legacy Implementation Initiatives ya ce tun bayan zaben shugaban kasar a 2015, mambobin kungiyar ke shawagi a kasar suna nema masa goyon baya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel