Tsinkiya ta tsinke! Jam'iyyar APC a jihar Kaduna tayi kaca-kaca da Gwamna El-rufai

Tsinkiya ta tsinke! Jam'iyyar APC a jihar Kaduna tayi kaca-kaca da Gwamna El-rufai

- Tsintsiya ta tsinke a jihar Kaduna

- 'Yan a ware na jam'iyyar APC a Kaduna sun caccaki Elrufa'I

- 'Yan a waren sun ce Elrufai ba tabuka komai ba

Bangaren jam'iyyar APC mai mulki da ta balle a jihar Kaduna dake a arewacin Najeriya da kuma basu ga maciji da Gwamnan jihar Malam Nasir El-rufai sun fito sunyi kaca-kaca da gwamnan.

Bangaren jam'iyyar da ke kiran kansa da suna APC akida sun ce gwamnatin jihar ta Kaduna bata tabuka komai ba har yanzu a cikin shekaru biyu da tayi tana mulkar jihar.

Tsinkiya ta tsinke! Jam'iyyar APC a jihar Kaduna tayi kaca-kaca da Gwamna El-rufai

Tsinkiya ta tsinke! Jam'iyyar APC a jihar Kaduna tayi kaca-kaca da Gwamna El-rufai

NAIJ.com ta samu labarin cewa shugaban jam'iyyar ta bangaren APC akida Mista Tom Maiyashi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wata fira da ya yi da yan jarida.

Tom Mai Yashi ya ce kuma ba komai a cikin mulkin Gwamnan jihar sai yaudara da karerayi.

Wadanda suka halarci taron sun hada da fitaccen da siyasar nan Isah Ashiru, Sanata Shehu Sani, Sule Buba, Yaro Makama, da shugaban gidan Talabijin din Liberty, Tijjani Ramadan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel