EFCC sun turo yan bindiga su kashe ni, kuma suka sa na’urar bincike a waya ta-Patience

EFCC sun turo yan bindiga su kashe ni, kuma suka sa na’urar bincike a waya ta-Patience

-Patience ta zargi EFCC da sunyi kokarin kashe ta har sau biyu amma bas u samu nasara ba

-Bayan EFCC akwai wasu hukumomin gwamanti da suke damu rayuwa na kaman FIRS da NDLEA

-Patience tayi kira da yan majalisan kasan da su ceceta kafin hukumomin su samu nasara halakata

EFCC sun turo yan bindiga su kashe ni, kuma suka sa na’urar bincike a waya ta-Patience

Uwargidan tsohon shugaban kasa Patience Jonathan

Uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta zargi hukuman EFFC da baiwa yan bindiga kwangilar hallakata.

Mrs jonathan ta ce so biyu suna kai ma rayuwanta hari basu samu nasara ba. Tana kira da yan majalisa dattawa da su bata kariya kafin abin ya wuce gona da iri har hukuman su samu nasaran kasheta.

KU KARANTA:Ali Ndume yayi barazanar maka FG a kotu

A wani wasika da lauyan ta ya rubuta Granville Abibo(SAN)&Co Mrs Jonathan ta ce” Sau biyu hukuman EFCCS su ka kai mata hari a cikin shekeran nan tun daga watan febrairu zuwa Afrilu 2017 akan. hanya Yenagoa-Mbaimu Road, jihar Bayelsa."

Patience ta zargi hukuman da sa nauran bincike a layin waya ta. Kuma suna turo mata wasiko na barazana dan tsoratar da ita.

Urwargidan tsohon shugaban kasan ta ce har da layin wayoyi yan uwanta da abokan arziki basu bari ba .kuma bayan haka hukuman EFCC na tura mata sako na tsoratarwa.

Bayan EFCC, hukumar FIRS suna cikin masu damu na.Cikin wata biyu da suka wuce hukumar FIRS sun shugu otel dina dake jihar Bayelsa sukayi mun barna ciki.

Haka yakara faruwa a wani shagon babban amini na Mr Aridolf Jo Resort dake Kpansia Expressway Bayelsa. Yan hukumar FIRS suka shiga ba tare da izinin kotu ba, suka barnatar da kayan cikin shagon a dalilin wai ba biya haraji ba

Ta kara dacewa bayan sun kulle mata asusun banki dinta na banki. Ba su tsaya a anan sai suka kara da rufe account din yan uwanta. Harda account din da suke amfanin dashi na kungiya mai zaman kanta, dan taimaka ma al umma.

Kuma hukumar sun kwace kadarori malakar kungiyoyin masu zaman kansu da ta kaddamar dan taimakon jama’a.

Manema labarai sun tuntubi mai Magana da yawon EFCC ,Mr Wilson Uwujaren akan zargi da Patience tayi akan su. Amma yaki yin Magana akan zargin.

Bayan haka hukumar yaki da miyagun kwayoyi NDLEA sun ce zargi da Patience ke musu na takura mata karya ne. basu da wani alaka da ita.

Mrs Jonathan ta kai karar EFCC da NDLEA zuwa majilssan dattijai akan matsi da takura da suke mata.

Wani shugaban hukuman NDLEA Mr Mitchel Oyefu yace zargin da Uwargidan tsohon shugaban kasa tayi musu bashi da asali kuma abin kunya ne kuma zai iya mutane su samu mumuna fahimtar hukuman.

Hukumar NDLEA sunce aikin su shine kama mutane da ke mu’amala da miyagun kwayoyi da masu samar da kwayoyin kuma su masu jajirce akan aikin su. Duk wanda suka kama da wani laifi zasu kama shi kuma a gurfanar dashi duk girmanshi ko matsayin a alumma.

Ku biyo mu a: https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel