Boko Haram: Zan maka Gwamnatin Buhari kotu - Sanata Ali Ndume

Boko Haram: Zan maka Gwamnatin Buhari kotu - Sanata Ali Ndume

- Sanata Ali Ndume ya ce zai kai gwamnatin tarayya kara

- Sanatan yace ba'ayi mashi adalci ba

- Sanatan dai yanzu haka yana fuskantar ladaftarwa ne

Jajirtaccen Sanatan nan mai wakiltar daya daga shiyoyin jihar Borno Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa yana nan yana nazarin kai gwamnatin tarayya kara a kotu bisa zargin kazafin da tayi masa.

Sanatan wanda wata babbar kotu ta wanke daga dukkan zargin da akeyi masa ya kuma ce kafafen yada labaran Najeriya ma dai basuyi masa adalci ba musamman ma yadda suka rika alakanta shi da kungiyar nan ta Boko Haram.

Boko Haram: Zan maka Gwamnatin Buhari kotu - Sanata Ali Ndume

Boko Haram: Zan maka Gwamnatin Buhari kotu - Sanata Ali Ndume

NAIJ.com ta samu labarin cewa dai a zaman yanzu Ndume dai ya na kan ladabtarwar dakatarwa ta tsawon watanni shida da majalisar tarayya ta yi masa, sakamakon kira da ya yi cewa a binciki shugagan majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kuma Dino Melaye.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel