Jam'iyyar APC ta kafa kwamiti don yiwa kundin tsarin ta garambawul

Jam'iyyar APC ta kafa kwamiti don yiwa kundin tsarin ta garambawul

- APC na shirin gyara tsarin mulkin ta

- Jam'iyyar ta kafa kwamitin da zaiyi aikin

- Gwamnan Bauci ne shugaban kwamitin

Jam'iyyar APC ta kafa kwamiti mai karfi da zai sake dubawa da bita da nazari da kwaskwarima da gyaran kudin tsarin jam'iyyar.

Gwamnan jihar Bauchi dake arewa-maso gabas din Najeriya ne dai zai shugabanci kwamitin watau Barista Muhammed A Abubakar.

Jam'iyyar APC ta kafa kwamiti don yiwa kundin tsarin ta garambawul

Jam'iyyar APC ta kafa kwamiti don yiwa kundin tsarin ta garambawul

NAIJ.com ta samu labarin cewa sauran mambobin kwamitin sun hada da Gwamnan Benue, Mista Samuel Ortom, da shugabannin jam'iyyar kamar su Muiz Banire, Sen. Francis Alimikhena, Alh. Inuwa Abdulkadir da dai sauransu.

Kawo yanzu dai mutane yan Najeriya sun zura ido suga wane irin gyare-gyare ne za'a fito dasu a tsarin na jam'iyyar ganin cewa tuni har ta fara rage farin jini a idanun talakan da ya jajirce don ganin ya zabe ta a zaben da ya gabata.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel