Munafukan miji na za su gane kuren su idan ya dawo - inji Aisha Buhari

Munafukan miji na za su gane kuren su idan ya dawo - inji Aisha Buhari

- Aisha Buhari tayi magana kan lafiyar mijin ta

- Asiha Buhari tace Allah ya anshi addu'ar talakan Najeriya

- Uwar gida Aisha Buhari tace Buhari na nan dawowa nan ba da dadewa ba

Uwar gidan shugaba Buhari watau Aisha Muhammadu Buhari ta yiwa yan Nigeria musamman ma talakawan dake yi masa addu'a ba dade ba rana albishir a karon farko cewa Allah ya karbi add'uoin su game da rashin lafiyar na mijinta Muhammadu Buhari.

Uwar gidan ta shugaba Buhari Aisha Buhari tace shugaba Buhari ya samu sauki a don haka suna godiya ga yan Nigeria bisa dumbin addu'oin da sukeyi masa na neman sauki.

Munafukan miji na za su gane kuren su idan ya dawo - inji Aisha Buhari

Munafukan miji na za su gane kuren su idan ya dawo - inji Aisha Buhari

NAIJ.com ta samu labarin cewa matar shugaban kasar a shafinta na Facebook tana fadi cikin zaurance cewa da zaran shugaban kasar ya dawo zai yi waje da 'yan tsirarun mutanen nan da suka mamaye gwamnatinsa suke hana ruwa gudu.

Tun farko dai Sanatan dake wakiltar shiyyar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani shine ya fara yin rubutun na zaurance a shafin sa na Facebook.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel