An kama wani katon barawon wayar salula da kayan mata a jihar Neja

An kama wani katon barawon wayar salula da kayan mata a jihar Neja

- An kama katon barawo a jihar Neja

- Barawon dai yana shigar mata ne sanye da hijabi

- Kasurgumin barawon yana anshe ma mutane wayar salula ne

Labarin da ke zuwa mana ba da dadewa na nuna cewa an kama wani kasurgumin barawon wayar hannu ta salula wanda kuma yake yin shigar mata a garin Minna dake zaman babban birnin jihar Neja.

Mun dai samu wannan labarin ne daga wani ba'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ta Facebook mai suna Jonpaul Oshioke Umoru wanda ya ayyana hakan a shafin sa na sada zumuntar na Facebook.

An kama wani katon barawon wayar salula da kayan mata a jihar Neja

An kama wani katon barawon wayar salula da kayan mata a jihar Neja

NAIJ.com har ilayau ta tattaro daga majiyar tamu cewa ma'abocin kafar ya dora wasu hotunan da aka dauka na barawon dauke da makamin sa sanye da hijabi mai kalar miyon goro.

Tuni dai an mutanen unguwa suka mika barawon zuwa ga hannun yan sanda bayan ya gama shan dukan tsiya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel