Mummunar cutar nan mai kisa ta zazzabin Lassa da sake bulla a Arewacin Najeriya

Mummunar cutar nan mai kisa ta zazzabin Lassa da sake bulla a Arewacin Najeriya

- Zazzabin Lassa ya sake bulla a Arewa

- Zazzabin ya bulla ne a jihar Plateau

- Har an samu mutuwar mutum 1

Mummunan labarin da muka samu yana nuna mana cewa cutar nan mai kisa cikin kankanin lokaci ta zazzabin Lassa ta sake bulla a Arewacin kasar nan a karamar hukumar Langtang ta jihar Plateau.

Mun dai samu labarin cewa cutar tuni har tayi sanadiyyar mutuwar wani yaro matashi dake a wata makarantar kwana ta Gwamnatin tarayya ta karamar hukumar.

Mummunar cutar nan mai kisa ta zazzabin Lassa da sake bulla a Arewacin Najeriya

Mummunar cutar nan mai kisa ta zazzabin Lassa da sake bulla a Arewacin Najeriya

NAIJ.com ta samu labarin cewa kwamishinar lafiya na jihar mai suna Kuden Deyin ya gasgata wannan batun yayin da yayi fira da kamfanin dillacin labaru na News Agency of Nigeria (NAN) a turance.

Mun dai samu labarin cewa Kwamishinan na lafiya na jihar yace: “Kwarai kuwa an samu barkewar zazzabin Lassa a Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Langtang; Zazzabin ya yi sanadiyyar rasa yaro daya, biyu kuma na kwance a asibi a halin yanzu”.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel