Dangote ya bada tallafin miliyan 50 ga wadanda rikicin Ile-Ife ta shafa

Dangote ya bada tallafin miliyan 50 ga wadanda rikicin Ile-Ife ta shafa

- Alhaji Aliko Dangote ya bada tallafin kudi naira miliyan 50 ga wadanda rikicin da ta barke a Ile-Ife ta shafa

- Dangote ya bada kyautar a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli a fadar Ooni na Ife

- Ogunwusi ya kalubalanci masu hannu da shuni da su yi kwaikwayi da Dangote ta hanyar agaza wa al’umma

Babban hamshaki dan kasuwan nan Alhaji Aliko Dangote kuma shugaban kamfanonin Dangote Group, ya bayar da tallafin kudi naira miliyan 50 ga wadanda rikicin kabilanci da ta barke a Ile-Ife da ke Jihar Osun ta shafa a ranar 8 ga watan Maris da ta gabata.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar Dangote ya bada wannan kyautar ne a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli a fadar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi.

Wannan rikicin kabilanci dai tsakanin Yarabawa da Hausawa mazauna garin Ile-Ife ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Dangote ya bada tallafin miliyan 50 ga wadanda rikicin Ile-Ife ta shafa

Wani bangaren da rikicin ta shafa a Ile-Ife

Dangote wanda babban darakta na Gidauniyar Dangote, Mrs. Suera Yusuf ta wakilta, ya ce cewa za a raba miliyan 50 a tsakanin mutane 220 da rikicin ta shafa.

Daraktan ta kira ga hadin kai tsakanin Yarabawa da Hausawa mazauna Ife cewa, zaman lafiya da hadin kai kawai zai iya kawo ci gaban al’umma.

KU KARANTA: Dangote baya tattalin dukiya - Seun Kuti

Ogunwusi, a jawabinsa ya gode ma Dangote ga karimcin wanda ya bayyana a matsayin abin alfahari.

Ogunwusi ya kalubalanci 'yan Najeriya masu hannu da shuni da su yi kwaikwayi da Dangote ta hanyar agaza wa al’ummar kasar.

Yayin da yake nasa bayani, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido, ya yaba jagorancin Ooni na Ife a kan matakin da ya dauka a lokacin rikicin.

Lamido ya gargadi ‘yan Najeriya masu furta kalaman nuna kyama da kiyaya cewa tattaunawa shine mafi amfani wajen warware duk sabanin ra'ayi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel