An kama wani mai gadi bisa zargin sace man fetur lita 10,000

An kama wani mai gadi bisa zargin sace man fetur lita 10,000

- An gurfanar da wani mai gadi a gaban kotun kan zargin sace man fetur

- Ana zargin mai gadin ne da laifuka biyu na hadin kai da kuma sata

- Kotu ta bada belin mutumin a kan kudi 200,000

Wani mai gadi mai shekaru 38 da hahuwa wanda aka sani da Lucky Uhunmunamure, wanda ake zargin ya saci lita 10,000 na man fetur na mai gidansa mai darajan kudi naira miliyan 1.4.

An gurfanar da wannan mai gadi ne a gaban kotun Tinubu Majistare da ke Legas a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli.

Uhunmunamure wanda bai da wani takamamman adireshin, yana fuskantar cajin laifuka biyu na hadin kai da kuma sata.

Mai gabatar da karar, Insp. Ben Ekundayo, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin a ranar 26 ga watan Afrilu a yankin Ikorodu da ke jihar Legas.

KU KARANTA: An cigaba: An kirkiro wayar da ba ta aiki da batiri

Ekundayo ya ce mai gadin ya hada baki da wasu wadanda yanzu haka ba san inda suke ba don sata lita 10,000 na man fetur wanda mallakar kamfanin Javy Investment Nigeria Ltd.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Uhunmunamure ya musanta zargin laifin.

Alkalin Kotun Majistare, Mista Ade Adefulire ya bada belin wanda ake tuhuma a kan kudi 200,000. Kotun ta kuma dage sauraran karar har zuwa ranar 25 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel