Kaduna: An samu karin masu rajistar kada kuri’a 40,317 a Kaduna

Kaduna: An samu karin masu rajistar kada kuri’a 40,317 a Kaduna

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da samu masu rajistar kada kuri’a 40,317 a Kaduna

- INEC ta yi karin cibiyoyin rajistar guda 8 a Kaduna

- Dazang ya ce za a fara rijistar a wadannan ƙarin cibiyoyin daga ranar Litinin, 10 ga watan Yuli zuwa 11 Agusta

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a Jihar Kaduna, a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli ta ce zuwa yanzu ta yi rajista mutane masu kada kuri'a 40, 317 a cikin shirin cigaba da rajistar masu kada kuri’a.

NAIJ.com ta tuna da cewa an fara rajistar masu kada kuri’a ne a fadin kasar a ranar 27 ga watan Afrilu 27 domin zaben shekarar 2019.

Ana gudanar da rajistar ne a hedkwatar kananan hukumomin 774 da ke fadin kasar wanda ana sa ran za a kawo karshe watanni biyu kafin zaben 2019.

Kaduna: An samu karin masu rajistar kada kuri’a 40,317 a Kaduna

Jami'an hukumar zabe mai zaman kanta shiyar jihar Kaduna; Tushen hoto: today.ng

A lokacin da yake jawabi da 'yan jarida a ranar Litinin jim kadan bayan wani taro da masu ruwa da tsaki, Mista Nick Dazang sakataren gudanarwar hukumar a jihar, ya ce an yi ƙarin cibiyoyin masu rajistar kada kuri'a' guda 8 don magance kalubalen da ake samu ta hanyar cunkoso da nisan cibiyoyin rajistar da wasu ke fuskanta.

KU KARANTA: Nasarar PDP a zaben jihar Osun farkon karshen jam’iyyar APC a Najeriya - Inji 'yan majalisar PDP

Sakataren ya bayyana cewa hukumar ta yi ƙarin cibiyoyin rajista 302 a fadin kasar gaba daya.

Sabin cibiyoyin zasu yi rajistar masu kada kuri’a har zuwa ranar 11 ga watan Agusta, sa nan kuma za a rufe su. A cewar Dazang

An yi sabin cibiyoyin ne a Rigasa, Gonin Gora, Tudun Nupawa, Ungwan Shanu, Ladduga, Gidan Waya, Katugal da Kwarbai 'B'.

Dazang ya ci gaba da cewa: “ Za a fara rijistar a wadannan ƙarin cibiyoyin daga ranar Litinin, 10 ga watan Yuli inda kuma za a kawo karshen rajistar a watan Agusta 11, 2017”.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel