Rundunar Sojin Najeriya za ta karasa lallasa ‘Yan Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya za ta karasa lallasa ‘Yan Boko Haram

- Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da wani sabon shiri

- Ana kokarin gamawa a Boko Haram a Arewa maso gabas

- Kwanan nan sama da ‘an ta’adda 700 su ka mika kan su

Rundunar Sojin Najeriya za ta karasa lallasa ‘Yan Boko Haram da su kayi saura a Dajin nan na Sambisa Inji Shugaban Sojin Najeriya Lafana Janar Tukur Buratai.

Rundunar Sojin Najeriya za ta karasa lallasa ‘Yan Boko Haram

Shugaban Rundunar Sojin Najeriya Buratai

Janar Tukur Buratai ya bayyana wannan ne a karshen makon can yayin da yake kaddamar da wani aiki a Jihar Kogi. Buratai ya sa wa wannan namijin aiki da za ayi ‘Operation deep punch’ watau kamar wani bugu mai fasa mummuke.

KU KARANTA: Fastocin Kudu sun soki Gwamnatin Buhari

Rundunar Sojin Najeriya za ta karasa lallasa ‘Yan Boko Haram

Sojoji za su karasa gamawa da Boko Haram

Manjo Janar R.O Yusuf wanda ya wakilci Shugaban hafsun Sojin Najeriya Janar Tukur Buratai yake cewa za su ga bayan ‘yan ta’addan Boko Haram da su ka rage a Dajin Sambisa domin a cigaba da tafiyar da al’amura a Yankin.

Kun ji cewa Shugaban Kasar Amurka Donald Trump yace idan ta kama sai ya kai wa Koriya ta Arewa hari don ya taka masu burki wajen makami mai linzamin da su ke harbawa har zuwa Kasar Amurka.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da rikicin Yaki Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel