Ta'addanci: Dakaru sun kama makaman yaki

Ta'addanci: Dakaru sun kama makaman yaki

- Za’a kawo karshen yaduwar makamai

- An kama kaso babba daga wajen masu kiwon shanu

- Batalliyar sojoji sun yi shirin tarwatsa makaman

Rundunar sojojin kasa na Najeriya sun yi shirin kawo karshe wasu makaman yaki sama da guda 600 da aka kama a wajen masu kiwon shanu da wadansu ‘yan ta’adda a sassa daban-daban a kasar nan.

Jaridar Sun sun ruwaito cewa za a tarwatsa wannan makaman ne a jihar Katsina a ranar Litinin 10 ga watan Yuli wanda gwamnan jihar Aminu Masari zai halarta da wasu kusoshin gwamnati.

Ta'addanci: Dakaru sun kama makaman yaki

Ta'addanci: Dakaru sun kama makaman yaki

Shugaban kungiyar hana yaduwar makamai Emmanuel Ihome yace akwai sama da makamai kimanin miliyan 690 a suna yawo a hannun wadanda basu dace su rike su ba. Yace idan aka bi diddigi akwai kimanin miliyan 8 a yammacin Afirka.

KU KARANTA: Munafukan miji na za su gane kuren su-inji Aisha Buhari

Yace wannan ba ana aka tsaya ba domin akwai zabbabun jihohi kamar: Kaduna, Kebbi, Sokoto, Zamfara, Cross rivers da Akwa Ibom wanda suma za a je a kafa wannan yakin domin hana yaduwar makamai.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel