Goyon baya - Rashin lafiyar Buhari ba matsala bace

Goyon baya - Rashin lafiyar Buhari ba matsala bace

- Rashin lafiyar Buhari ta kawo cikas

- Mukaddashin shugaban kasa yayi doguwar tattaunawa da manema labarai

- Kungiyar yaki da rashawa sun bayyana ra'ayinsu

A ranar litinin 10/Yuli/2017, kungiyar yaki da rashawa, Anti-corruption & Research- Based Data Initiative (ARDI) suka bada goyon banyansu kasancewar rashin lafiyar shugaba baza ta kawo cikas a tafiyar tasu ba.

Sakataren kungiyar, Mr.Dennis Aghanya ne ya bayyanawa masu daukan rahoto a jihar Legas. Yace kungiyar tasu za tayi nasara akan yaki da rashawa data sa a gaba sannan kuma yana wa shugaba Buhari fatan samun waraka.

Aghanya ya cigaba da bayyanawa manema labarai cewa, musabbabin abinda yake janyo mana koma baya a kasar nan shine cin hanci da rashawa. Amma matukar kowa ze cire son zuciyar shi domin a samu a kawar da wannan matsala, to lallai za a samu canji da kuma cigaba a kasar nan.

Goyon baya - Rashin lafiyar Buhari ba matsala bace

Goyon baya - Rashin lafiyar Buhari ba matsala bace

Sakataren ya kara da cewa, tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta dauko akan yaki da rashawa,tabbas idan aka bisu za a yi nasara. Yace kamar tsarin da ta dauko wanda tace za a sake yin hukunce-hukuncen da zata daukarwa dukkan wani mai satar mutane da neman kudin fansa, fashi da makami da ma dukkan wani me ta’addanci a kasar nan.

KU KARANTA: Dangote baya tattalin dukiya-Seun Kuti

Rahotanni daga kafofin yada labarai sun ruwaito cewa mukaddashin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a makon da ya gabata a babban birnin Abuja. Yace za a gayyato dukkan manyan shugabannin ‘yan sanda wadanda suka yi ritaya domin su bada gudunmawar su dan gane da irin fasaha da hangen nesan da suka samu a lokacin da suke aiki.

Mukaddashin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci bikin kaddamar da wani littafi ne a birnin tarayya me taken “Dokokin hanawa da gano laifuka na jami’an ‘yan sanda.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel