Arewa su ka hana Kasar nan cigaba Inji Kungiyar Afenifere

Arewa su ka hana Kasar nan cigaba Inji Kungiyar Afenifere

- Kungiyar Afenifere ta zargi Arewa da hana ruwa gudu a Kasar nan

- Afenifere tace Arewa ba ta so sauran Yankin kasar su cigaba

- Wasu da dama dai su na kira ayi wa Kasar garambawul idan har ana so a cigaba

Wata Kungiya mai suna Afenifere ta Kudancin Kasar nan ta zargi Yankin Arewa da hana ruwa gudu idan aka zo maganar yi wa Kasar nan garambawul.

Arewa su ka hana Kasar nan cigaba Inji Kungiyar Afenifere

Hoton wani Shugaban Kungiyar Afenifere

Mai magana da bakin Shugaban Kungiyar Yinka Odunmakin yace manyan Arewa ke kokarin danne sauran Yankin kasar a ko yaushe duk da cewa idan an raba kasar babu wanda zai sha wahala ko kadan.

KU KARANTA: Osinbajo ya kai ziyara Jihar Neja

Arewa su ka hana Kasar nan cigaba Inji Kungiyar Afenifere

Hoton Osinbajo da manyan Arewa a Aso Villa

Jama'a da dama a Najeriya dai yanzu su na kira a sauya tsarin kasar inda kowane Yanki zai kara karfi ya kuma rage dogaro da wani ko kuma Gwamnatin Tarayya. Da dama dai an dogara da man fetur din da ke Kudancin kasar ne.

Kungiyar manyan Kiristocin kasar nan ta nuna goyon bayan ta na ayi wa Kasar garambawul sannan kuma ta kira sauran Fastocin kasar su rika sa baki duk lokacin da su ka ga za a cuce su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon Fafutukar Biyafara zuwa yanzu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel