Tsarin ilmi: Kiristoci sun soki Gwamnatin Muhammadu Buhari

Tsarin ilmi: Kiristoci sun soki Gwamnatin Muhammadu Buhari

- Kiristocin Najeriya sun soki tsarin ilmi na Gwamnatin Shugaba Buhari

- Gwamnatin Shugaban kasa Buhari ta dabbaka wasu sauye-sauye a tsarin Boko

- Wasu Fastocin kasar su na ganin da su ake a wannan shirin

Kungiyar Kiristocin Najeriya sun soki tsarin ilmi na Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ganin an hade ilmin Addinin Kirista da wani darasin.

Tsarin ilmi: Kiristoci sun soki Gwamnatin Muhammadu Buhari

Hoton wani Fasto tare da Muhammadu Buhari

Wasu Fastoci na Kudancin Kasar sun soki wannan tsari da aka dabbaka kwanan nan duk da cewa tun lokacin Shugaban kasa Goodluck Jonathan aka kawo wannan tsari. Tuni dai Gwamnatin nan tayi wannan bayani.

KU KARANTA: Tarihin Kungiyar Izala a Najeriya

Tsarin ilmi: Kiristoci sun soki Gwamnatin Muhammadu Buhari

Fastoc tare da Shugaba Muhammadu Buhari

Kungiyar ta kuma nuna goyon bayan ta na ayi wa Kasar garambawul sannan kuma ta kira sauran Fastocin kasar su rika sa baki duk lokacin da su ka ga za a cuce su. Kiristocin dai sun yi wa Shugaba Buhari addu’a a taron.

Kwanaki Kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya tayi kira da Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya duba wannan mataki da Buhari ya dauka na soke addinin Kirista daga darasin makarantu, su kace amma an bar darasin Arabi da Musulunci.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mai burodi ta zama mai kudi a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel