Wani babban tirela ta hafka kan wasu mutane a Ughelli

Wani babban tirela ta hafka kan wasu mutane a Ughelli

- Wani tirela ta rugurguje wasu motoci yayin da ya saki hanya a ga Ughelli

- Babban motar da ta yi hatsarin nada lamda CC 1586i

- Kwamandan ta FRSC ya ce bai da masaniya a kan ko akwai wanda ya mutu a hadarin

Akalla mutum daya ya mutu yayin da wasu 8 suka jikkata a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli a lokacin da wani babban mota IVECO ta saki hanya zai ram cikin masu tafiya da kafa a bakin hanyar da kuma ‘yan acaba a garin Ughelli da ke jihar Delta.

Rahotanni sun nuna cewa motar tirela mai lamba CC 1586i ta saki hanya ne tun a mararrabar Otovwodo da ke babban hanyar gabas zuwa yamma na garin inda ya buge wasu ‘yan acaba da kuma wasu motoci da aka fakin ta gefen hanya.

NAIJ.com ta tattaro cewa, a lokacin da yake tabbatar da hadarin, babban kwamandan ta FRSC, Mista Olusola Olusegun, ya ce ‘yan acaba biyu da hatsarin ta rutsa da su a dai dai karfe 10:40 na safe an kai su zuwa asibitin tsakiyan Ughelli.

KU KARANTA: Yan sanda 4 sun gamu da gamon su bayan da suka cuci wani bawan kudi N50,000

Kwamandan ya ce: " Ban da masaniya a kan wani mutuwa yanzu, amma mutanen da aka kai asibiti na cikin mawuyacin hali yanzu haka”.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel