Rundunar sojin ƙasa ta samar da motocin yaƙi da aka ƙera a gida Najeriya

Rundunar sojin ƙasa ta samar da motocin yaƙi da aka ƙera a gida Najeriya

- Rundunar Sojin kasa ta kaddamar da ginin katafaren sansanin Sojoji

- Babban hafsan Soji, Buratai ya sanya ma sansanin suna Muhammadu Buhari

Rundunar Sojin kasa ta kaddamar da wasu motocin yaki da aka hada su a nan gida Najeriya, babban bako a yayin bikin kaddamarwar shine ministan tsaro, Mansur Dan-Ali.

Baya da kaddamar da motocin, har ila yau, ministan ya sanya tubalin sansanin sojoji na musamman da rundunar zata gina wanda aka sanya ma suna Muhammadu Buhari cantonment.

KU KARANTA: Ke Duniya: Matashi ya hallaka abokinsa ta hanyar farke masa ciki don ya kwashi kayan cikinsa (HOTUNA)

Shi dai wannan sansani an jibge shi ne a garin Giri,dake wajen babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Rundunar sojin ƙasa ta samar da motocin yaƙi da aka ƙera a gida Najeriya

Buhari sanye da kayan rundunar sojin ƙasa

A nasa jawabin, babban hafsan sojin kasa, Tukur Buratai yace jami’an rundunar sojin ne suka kera wadannan motoci bayan kwashe dogon lokaci suna gudanar da bincike, inji majiyar NAIJ.com.

Buratai ya kara da cewa sun samar da sansanin ne domin habbaka ayyukan Soji, musamman ta fannin yaki da Boko Haram, inda ya kara da cewa tuni an aika da motocin zuwa Arewa maso gabas.

Rundunar sojin ƙasa ta samar da motocin yaƙi da aka ƙera a gida Najeriya

Rundunar sojin ƙasa

Dayake nasa jawabin, minista Mansur Dan Ali yace sun dukufa wajen inganta ayyukan rundunar Sojin kasa ta hanyoyi guda 3 da suka hada da horar da jami’anta, sauyi da kuma tabbatar da walwalar sojoji.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Menene ra'ayin yan Najeriya game da mulkin Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel