Ra'ayi: Awakai da kaji sun fi Yesu - Tsohon Fasto

Ra'ayi: Awakai da kaji sun fi Yesu - Tsohon Fasto

- Tsohon Fasto ya bayyana ra'ayin shi

- Fasto ya canja abin bauta

- Wani Fasto yace ya gano gaskiya

Wani tsohon Fasto Onyeozi Nwolisa ya bayyana ra'ayin shi a sarari a shafin facebook da cewa yafi ganin kimar wasu dabbobin akan Yesu.

A shekarar da ta gabata, shafin Naij.com sun gabatar da Onyeozi Chukwunonso Obijiofor Nwolisa. Wannan tsohon Fasto wanda a yanzu ya koma addinin gargajiya yace yanzu abin bauta shine 'Chukwu Okike Abiama' ba Yesu ba.

Wannan tsohon Faston ya fito fili a ranar lahadi 9/Yuli/2017 inda ya bayyana hoton kanshi, wata akuya da kaza da kuma wasu ganyen itatuwa wanda yake ganin sun fi Yesu.

Ra'ayi: Awakai da kaji sun fi Yesu - Tsohon Fasto

Wani tsohon Fasto ya ce awakai da kaji sun fiye masa Yesu

Ya bayyana ra'ayin shi da cewa "babu wani me jan kunne da zai zo ya sake ce masa ya cigaba da bautar Kuros domin kuwa yanzu ya gano gaskiyar abin bauta da kuma sadaukarwa wanda ya fi Yesu a gurin shi."

KU KARANTA: Sanata Ndume - Boko Haram sun kai makura

Wadansu daga cikin mabiyanshi sun yi tir da wannan al'amari, baya ga wasu kuma suke shawartar shi akan abinda suke ganin shine daidai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel