Masari ya nemi masu zuba hannun jari a yankin ma'adinai

Masari ya nemi masu zuba hannun jari a yankin ma'adinai

- Gwamna Masari ya nemi masu zuba hannun jari a yankin ma'adinai

- Jahar tana da arzikin ma'adinai daban-daban

- Gwamnatinsa zata hada gwiwa ga masu saka hannun jari

Gwamnan Jahar Katsina, Aminu Bello Masari yace a binciken da Majalisar bincike da cigaban ma’adinai ta Kasa tayi ya nuna Jahar Katsina tana da albarkar yawan ma’adinai daban-daban da ba a sarrafa su.

Masari yayi maganar ne a taron da akayi na mahakan ma’adinai a Jahar ta hanyar mataimakinshi Mannir Yakubu. Yace: "a shirye suke da su bada hadin gwiwa da duk wanda ya shirya saka hannun jari don bincike da yadda za a sarrafa anfanin ma’adinan da arzikin da Jahar take dashi."

Masari ya nemi masu zuba hannun jari a yankin ma'adinai

Masari ya nemi masu zuba hannun jari a yankin ma'adinai

Masari ya tursasa masu ruwa da tsaki da su bada goyon baya wajen ganin manufar Gwamnati ta ci gaba bangaren ma’adinan. Ganin yadda aka samu raguwar shigowar kudade ta bangaren mai, yasa Kasa ta dage kan ganin an samu ta inda kudade zasu shigo ba lallai sai ta bangaren mai ba.

KUMA KU KARANTA: Duniya ina zaki damu, an tsinci wani jariri rufe a cikin kwali a makabartar Kaduna (Hotuna)

A dokar tsarin hako ma’adinai na Jahar na 2007: ya bada umarnin bude hanyar biyan kudaden da suke shigowa da za a samu daga bangaren hakan ma’adinai don tabbatar da gaskiya da daidaita karbar haraji.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel