Kungiyar dalibai na kasa zata gudanar da gagarumin zanga-zanga a Kaduna

Kungiyar dalibai na kasa zata gudanar da gagarumin zanga-zanga a Kaduna

- Kungiyar dalibai na kasa, NAN zata gudanar da gagarumin zanga-zangar lumana a Kaduna a watan Satumba

- Kungiyar ta ce wannan zanga-zangar wani bangare ne na nuna hadin kai matasan Najeriya

- Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta kawo karshen tashin hankali a kasar ta hanyar tattaunawa da matasan yankunan biyu

Duka daliban Najeriya, a karkashin kungiyar dalibai na kasar wato National Association of Nigeria Students, NANS, zasu fara wata gagarumin zanga-zangar lumana tsakanin Satumba 30 zuwa 3 ga watan Oktoba, dalibai zasu zauna ne a cikin garin Kaduna a wani rashin amincewa da wa’adin da wasu shugabannin matasan kungiyoyin arewa suka ba ‘yan kabilar Igbo da su fice daga sassa na arewacin Najeriya.

NANS ta ce wannan gangamin zaman lafiya da kuma hadin kai kasar, wani bangare ne na nuna hadin kai matasan Najeriya.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, kungiyar dalibai ta yi Allah wadai da kalmomin kiyayya da kuma yunkurin raba Nigeria, ta bayyana cewa, akwai dalibai a tsakanin kungiyoyi masu fafutukar kafa yankin Biyafara, aka zalika kuma akwai dalibai a tsakanin kungiyoyin matasan Arewa da suka ba kabilar Igbo wa’adin ficewa daga arewa, sabili da haka, kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta kawo karshen tashin hankali a kasar ta hanyar tattaunawa da kowane rukuni baki daya.

Kungiyar dalibai na kasa zata gudanar da gagarumin zanga-zanga a Kaduna

Kungiyar dalibai na kasa na shirin wata gagarumin zanga-zanga a Kaduna; Tushen hoto: vanguardng

KU KARANTA: Bamu yarda da tattaunawa da Osinbanjo yake yi ba - Samarin Ohanaeze

A wani taron manema labarai a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli a Enugu, shugaban kungiyar dalibai na kasa, Aruna Kadiri tare da jami’an kungiyar gaba daya a kasar sun nuna fargabar cewa matasan arewan zasu iya kai masu harin don haka sun bukaci hukumomin tsaro da su kare rayyuka da kuma dukiyoyin mutane.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel