Zahra Buhari ta yi sharhi a kan halin da mahaifinta ke ciki

Zahra Buhari ta yi sharhi a kan halin da mahaifinta ke ciki

- ‘Yar shugaban kasar Najeriya, Zahra Buhari ta yi magana akan lafiyar mahaifinta

- Shugaban kasar na a wajen kasar kusan watanni uku da suka wuce ba tare da wani tsayayyen nhujja kan halin da yake ciki ba

- Zahra ta buga wani rubutu a shafin Twitter inda ta bayyana cewa mahaifinta na nan cikin koshin lafiya

Kwanan nan Zahra Buhari Indimi ta bayyana halin da lafiyar mahaifinta yake ciki. Shugaban kasa Buhari na birnin Landan kusan sama da watanni uku inda yake samun kulawar likita kan wani rashin lafiya da ba’a bayyana ba. ‘Yan Najeriya sun shiga damuwa game da halin da shugaban kasa ke ciki sannan kuma kawai suna samun bayani ne a kan halin da yake ciki.

KU KARANTA KUMA: An bankawa tsintsiya wuta a yayin da ‘yan jam’iyyar APC 500 suka canza sheka zuwa PDP (hoto)

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari wacce a yanzu haka ta birnin Landan tare da mijinta batayi magana a kan lafiyarsa ba tukuna amma Zahra ta ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa yana cikin koshin lafiya a cikin wani rubutu da ta buga a shafinta na twitter.

Zahra ta buga wani rubuti yan mintoci kadan da suka shige a ranar Litini, 10 ga watan Yuli bayan ta gaishe da ‘yan Najeriya sannan kuma tayi yunkurin amsa tambaya game da mahaifinta daga ‘yan kasa da suka nuna damuwa.

Zahra Buhari ta yi sharhi a kan halin da mahaifinta ke ciki

Daga shafin Zahra na Instagram

A rubutun ta, ta bayyana cewa shugaban kasar na cikin koshin lafiya amma bata sanar da komai game da lokacin dawowarsa kasar ba. Ta ce: “Ina yini Najeriya. Yana nan lafiya” bayan an tambayeta yadda mahaifinta yake.

Zahra Buhari ta yi sharhi a kan halin da mahaifinta ke ciki

Daga shafin Zahra Buhari na twitter

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel