Shugaban musulunci yace yankin kudu maso gabas bazata dakatar da fafutukar Biyafara ba

Shugaban musulunci yace yankin kudu maso gabas bazata dakatar da fafutukar Biyafara ba

- Alhai Abubakar Orluelder, wani shugaban musulunci a jihar Rivers wanda ya maida martani ga al’amarin Biyafara ya ga laifin gwamnatin jam’iyyar APC da bata tsinana wani abun kwarai ba

- Orluelder yace geamnatin baya sukan yi amfani da lokaci gurin ci gaban Arewa amma wannan hgwamnatin bata tsinana ma kudu maso kudu da kudu maso gaban komai ba

- Shugaban na musulunci ya bayyana cewa abunda ya kamata gwamnatin tarayya tayi ma mutanen Biyafara shine ta yarda da sake fasalin al’amura domin koma ya zauna tare cikin lafiya

Alhaji Abubakar Orluelder, wani shugaban musulunci a jihar Rivers, ya sanar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa kudu maso gabas bazata janye daga fafutukar neman kasar Biyafara ba.

Alhaji Orluelder ya bayyana hakan ne a Port Harcourt a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli, yayinda yake magana a kan halin da kasar ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Atiku Abubakar ya kai ziyara ga gwamnan jihar Kano don ta’aziyar mutuwar Maitama Sule

Ya bayyana cewa idan ba’a sake fasalin al’amuran kasar a yankuna sidda ba, masu faftukar Biyafara bazasu gaza ba.

Daily Sun ta ruwaito cewa ya yi Allah wadai da abubuwan da wasu gwamnonin jiha suka furta game da Najeriya.

Shugaban musuluncin ya zargi gwamnatin APC da son kai gurin nade-naden makaman tarayya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel