Yankin Kudu: Ka kare mutanen mu a Arewa, ko... - Inji shugabannin kudancin Najeriya

Yankin Kudu: Ka kare mutanen mu a Arewa, ko... - Inji shugabannin kudancin Najeriya

- Shugabannin kudancin kasar sun yi taron gaggawa a jihar Legas da kuma jihar Enugu game da wa’adin da aka ba ‘yan kudu mazaunar arewa

- Shugabannin sun bukaci gwamnatin tarayya ta bayyana ma ‘yan Najeriya ta yadda zata kare ‘yan kudu da suke arewa

- Shugabannin sun kuma koka ta yadda kashe-kashen Fulani makiyaya ke karuwa a fadin kasar

Kafin wa’adin na watan Oktoba 1 da shugabanin kungiyoyin matasan arewa suka ba ‘yan kabilar Igbo da su fice daga arewacin kasar ya cika, shugabannin yankin kudancin kasar a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli sun gargadi Mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo da ya bayyana ma 'yan Najeriya shiri da tsare-tsaren gwamnati don kare ‘yan kudancin kasar dake zaune a Arewacin Nijeriya.

Shugabannin daga yankunan kudancin kasar uku sun hadu a Legas kamar yadda gwamnonin yankunan kudu maso gabas da kuma Kudu maso Kudu suka shiga wani taron a jihar Enugu domin a samu wata masaya a kan al'amurran da suka shafi mutanen su. Takwas daga cikin gwamnonin 11 daga yankuna biyu suka isa wajen taron kafin su fara tattaunawa a daren ranar Lahadi.

Shugabannin kudancin kasar da suka hadu a Legas sun yi gargadin cewa hari a kan wani kabila mazaunan jihohin arewa, toh, za a iya gani a matsayin hari ne ga duk ‘yan kudancin kasar.

Yankin Kudu: Ka kare mutanen mu a Arewa, ko... - Inji shugabannin kudancin Najeriya

Zaman taron gaggawan shugabannin kudancin Najeriya; Tushen hoto: vanguardng

Shugabannin sun kuma koka da yaduwar rikice-rikicen Fulani makiyaya a kudu da kuma sauran sassan kasar, inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta dauki mataki a kan al’amarin.

KU KARANTA: Cakwakiya a cikin gidan PDP: Ali Modu ya sake samun rinjaye akan Makarfi

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da; tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Obong Victor Attah, shugabannin kungiyar Afenifere, Ayo Adebanjo, Sanata Femi Okurunmu, Cif Supo Shonibare, tsohon babban darekta hukumar leken asiri na kasar (NIA), Cif Albert Horsfall, tsohon shugaban hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), Sanata Bassey Ewa-Henshaw, tsohon babban daraktan na NDDC, Mista Timi Alaibe, Mai kula dakungiyar Ijaw Monitoring Group, IMG, Joseph Evah, kakakin kungiyar Afenifere, Yinka Odumakin, Goddy Uwazurike, Olorogun M.O Taiga, da sauransu.

Horsfall: “ Ya ce dole ne Mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya sanar da ‘yan Najeriya ayyuka da kuma shirin gwamnatin tarayya ta hanyar kare ‘yan kudancin kasar da suke zaune a jihohin arewa daban daban”.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel