Aisha na bakin ciki da halin da Buhari ke ciki

Aisha na bakin ciki da halin da Buhari ke ciki

- Gidan jaridar yanar gizo, Sahara Reporters, ta yi ikirarin cewa anyi ma uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari iyaka da ganin mijinta a Landan

- Jaridar ta yi zargin cewa Aisha bata zama tare da mijinta a gidan Abuja a birnin Landan, amma dai tana zaune a wani gidan haya

- Shafin jaridar ta kuma yi ikirarin cewa shugaban kasar na cikin wani hali

Wani rahoto daga shafin jaridar yanar gizo, Sahara Reporters, ya yi ikirarin cewa anyi ma uwargidan shugaban kasa Aisha iyaka da ganin mijinta shugaba Muhammadu Buhari wanda ke jinya a birnin Landan.

NAIJ.com ta tuna cewa a ranar 2 ga watan Yuli, Aisha Buhari ta bar Abuja don ziyartan maigidanta dake jinya a birnin Landan, a cewar wata sanarwa daga Suleiman Haruna, daraktan bayanai na uwargidan shugaban kasar.

Amma Sahara Reporters ta rahoto sabanin cewa duk da Aisha na tare da mijinta a Landan, bata zama a gidan Abuja a Landan tare da mijinta, amma tana zaune ne a wani gidan haya.

KU KARANTA KUMA: Anyi gangamin fara yi ma ɗan majalisa Abdulmuminu Jibrin kiranye a garin Dakatsalle

Shafin tayi zargin cewa wani tsohon hoton Aisha da mijinta na yawo a yanar gizo ta yadda zai sa a zata matar shugaban kasar ta hadu da mijin nata.

Shafin jaridar ta kuma yi ikirarin cewa matar shugaban kasa na ziyartan Buhari ne kawai idan an barta.

Jaridar ta kuma bayyana cewa wata majiyar fadar shugaban kasa da aka boye sunanta ta bayyana cewa Aisha ta hadu da shugaban kasa inda suka ci abincin dare a ranar 9 ga watan Yuli, amma ta bar gurin cikin bakin ciki sakamakon rashin lafiyar shugaban kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel