Wadanda suka yi ma APC aiki basu amfana daga gareta ba - Oyegun

Wadanda suka yi ma APC aiki basu amfana daga gareta ba - Oyegun

- Cif Oyegun ya ce wadanda suka yi ma jam’iyyar APC aiki basu amfana daga gare ta ba

- Shugaban jam’iyyar y ace jam’iyyar na da bangarenci gurin yin sakayya

- Yace ya amsa kiraye-kiraye da dama daga fusatattun mambobi

Cif John Oyegun wanda ya kasance shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya nuna rashin jindadi kan nade-nade da akayi a lokacin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wata hira da jaridar Vanguard, shugaban jam’iyyar ya ce wasu mambobi na jam’iyya mai ci wadanda sukayi gwagwarmaya har aka kai ga nasara basu amfana daga gare ta ba.

Da yake maida martani ga wani tambaya, Oyegun yace akwai matsala gurin bada mukamai kamar yadda wandanda sukayi ma jam’iyyar aiki basu samu ladan aikinsu ba.

KU KARANTA KUMA: An bankawa tsintsiya wuta a yayin da ‘yan jam’iyyar APC 500 suka canza sheka zuwa PDP (hoto)

A halin da ake ciki, rahoto daga jaridar Punch ya nuna cewa shugabannin APC sun gana kan rikicin dake tsakanin fadar shugaban kasa da majalisar dattawa kan nadin shugaban EFCC, Ibrahim Magu.

A cewar rahoton, jam’iyyar ta sanya baki a rikicin sannan kuma zata kaddamar da matsayinta kafin karshen mako.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel