Kazafi: 'Yan sanda sunyi ram da wani malamin makaranta

Kazafi: 'Yan sanda sunyi ram da wani malamin makaranta

- Tsohon minista ya shigar da kara

- Malamin makaranta ya yi katobara

- ‘Yan sanda sun kama wani malamin makaranta

‘Yan sanda sun damke wani malamin makarantar sakandiri a jihar yobe, Muhammed Kime saboda wani kazafi da ya yi a shafin san a Facebook akan tsohon gwamnan jihar, sanata Bukar Abba da kuma tsohon minista mai kula da harkokin ‘yan sanda, Maina Waziri.

Malamin yace kawowa yanzu babu ko aiki daya da sanatan ya gabatar a majalisar dattawa domin a aiwatar musu a jihar tun daga lokacin da aka zabe shi.

Tsohon ministan beyi wata-wata ba, ya shigar da kara babbar hedi-kwatar ‘yan sanda akan abinda wannan malamin ya ruboto wanda sanadiyar hakan ne ‘yan sanda suka cafke shi a ranar Juma’ar da ta gabata.

'Yan sanda sunyi ram da wani malamin makaranta

'Yan sanda sunyi ram da wani malamin makaranta

Malamin wanda ya kammala karatun shi akan yaruka, ya ruboto cewa “mutanen nan guda biyu da kuka sani (Abba) da (Maina) mashayan giya ne. Ya kuma ce tunda aka zabi sanata Bukar ko bulo daya be kafa ba a mazabarsa.

Ya kara da cewa ya kamata a fara yunkurin tumbuke sanatan daga kujerar sa domin wanda ya cancanci kujerar ya hau, kuma idan hakan ta faru kada sanatan ya sake sanya kafar shi a Jihar Yobe domin jihar ta tsarkaka daga mutane irin shi.

KU KARANTA: Cakwakiya a cikin gidan PDP: Ali Modu ya sake samun rinjaye akan Makarfi

Mukhtar Aja wanda dan uwa ne ga wannan malamin, ya bayyanawa manema labarai cewa cikin karshen makon da ya gabata ne suka yi belin shi daga hannun ‘yan sanda a babban ofishin su na Damaturu.

Malamin ya bayyanawa manema labarai cewa abinda ake tuhumar shi dashi tabbas haka ne, kuma wannan abu tsautsayi ya faru akan shi wanda ake cewa baya wuce ranar sa. Ya kuma sake rubutawa a shafin facebook, yana me nadama da bada hakuri ga tsohon ministan Adamu Maina Waziri a bisa abinda ya fada akanshi, yana kuma shawartar al’umma da su yasar da wannan zancen.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel