Mugabe ya sake komawa Singapore duba lafiyarsa

Mugabe ya sake komawa Singapore duba lafiyarsa

- Robert Mugabe ya sake komawa Singapore duba lafiyarsa

- Wannan shine zuwansa na uku a cikin shekararnan

- Tun 1980 yake Shugaban Kasar Zimbabwe

Shugaban Kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ya sake komawa Kasar Singapore duba lafiyarsa. Wannan shine karo na uku da yaje duba lafiyarsa a cikin shekarar nan.

Mugabe ya bar Zimbabwe ne a ranar litinin don zuwa duba lafiyarsa da yake akan kari a Kasar Singapore tun bayan zuwansa na karshe a watan Maris.. Zai dawo a karshen mako don Janaizar tsohon Shugaban Joji Godfrey Chidyausiku.

Mugabe ya sake komawa Singapore

Mugabe ya sake komawa Singapore

Robert Mugabe tsoho ne, mai shekaru 93 a doron Kasa. Tun a shekarar 1980 ya fara mulkin Shugaban Kasar Zimbabwe, kuma zai sake tsayawa takara a zaben da zasuyi nan gaba.

KUMA KU KARANTA: Duniya ina zaki damu, an tsinci wani jariri rufe a cikin kwali a makabartar Kaduna (Hotuna)

Bacci ya kan sace idan suna tsakiyar taro, kuma yana da matsalar yin tafiya. Duk da shekarun da Mugabe yake da, bai hana kungiyar ZANU-PF tsaida shi a matsayin dan takararsu ba a zaben da zasuyi a shekarar 2018.

Sh ne Shugaban da yafi kowane Shugaba a duk fadin Afrika yawan shekaru. A shekar 2016 sai da Gwamnatin Kasar ta musanta jita-jitar da akayi na cewar ya mutu a Kasar Waje yayin da yaje hutu.

Tafiyarshi zuwa Singapore yayi ta ne bayan tafiytar shugaban Kasar Najeriya zuwa Ingila na biyu jinya a shekarar nan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel