Sanata Ndume: Boko Haram sun kai makura

Sanata Ndume: Boko Haram sun kai makura

- Sanata Ndume yayi kira ga gwamnatin Najeriya

- Boko Haram sun kai sabon hari Jihar Borno

- Ndume yace abin yana ci mana tuwo a kwarya

A ranar lahadin da ta gabata ne Sanata Ali Ndume yayi Allah wadai akan hare-haren da Boko Haram suke yi a Jihar Borno sanadiyar sabon harin da suka yi a jami’ar Maiduguri. Ya kuma ce wannan koma baya ne ga kasa Najeriya baki daya.

Sanatan na jam’iyar APC me wakiltar yammacin Jihar Borno wanda a yanzu haka yana kan dakatarwar da aka yi mishi a watannin baya, ya fadawa manema labarai cewa “da ace yana kan bakin aikin shi da ya nemi ganawa da shugabannin jam’ian tsaro domin yaji ta bakin su akan matsalolin da suke fuskanta wajen kawo karshen Boko Haram.

Yace yanzu Jihar Borno babu kwanciyar hankali kamar yadda aka saba saboda ire-iren hare-haren da ‘yan Boko Haram suke yi a Jihar yana tayarwa da jama’ar Jihar tasu hanakali. Yace da ba a dakatar dashi ba, da ya shigar da korafi a majalisa domin a gayyato shugabannin jami’an tsaro a tattauna dasu akan ibtila’in dake faruwa a Jihar.

Boko Haram sun kai hari jami'ar Maiduguri

Boko Haram sun kai hari jami'ar Maiduguri

Yace kudaden da gwamnatin Najeriya ta ware domin dawo da cigaban Jihohin da wannan abin ya shafa sunyi karanci. Sanatan ya na shawartar gwamnatin Najeriya akan ta tashi tsaye kuma ta sake nazari domin dawo da cigaban Jihohin arewa maso gabas na Najeriya.

KU KARANTA: Dan autan sayayyan Man Utd Lukaku zai gurfana a gaban Kotu

Ndume yace idan aka dubi tallafin da kasashen waje suka bayar na kudi Naira Biliyan 245 aka hadashi da wanda gwamnatin Najeriya ta bayar Naira Biliyan 45 sai a ji kunya domin aiyukan da za ayi a ba kadan bane saboda irin koma bayan da Jihohin suke fuskanta na zamantakewar rayuwa.

A karshe Ndume yana yabon gwamnatin Najeriya akan tallafin da take bayarwa wajen ciyar da jama’ar da suke sansanin gudun hijira wanda ibtila’in na Boko Haram ya afka musu.Yana kuma jinjinawa sojojin Najeriya akan irin gudunmarwar da suke bayarwa domin kawo karshen wannan annoba.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel