Dan autan sayayyan Man Utd Lukaku zai gurfana a gaban Kotu

Dan autan sayayyan Man Utd Lukaku zai gurfana a gaban Kotu

- Sabon Dan kwallon Man Utd zai gurfana a gaban Kotu nan gaba

- Ana zargin Dan wasan da takurawa mutane cikin tsakiyar dare

- Wannan abin ya faru ne Birnin Los Angeles na Amurka

Sabon Dan wasan da Kungiyar Manchester United ta sayo daga Everton Romelu Lukaku ya shigo da kafar hagu don kuwa ya fada a hannun Hukuma.

Dan autan sayayyan Man Utd Lukaku zai gurfana a gaban Kotu

Sabon Dan wasan Man Utd da Kocin sa a Chelsea

Dan wasan gaban dai yana Kasar Amurka inda Likitocin Kungiyar Manchester United su ke duba lafiyar sa. A Birnin Los Angeles din ne Dan wasan su ka shiga cashewa cikin dare inda su ka addabi Jama'a.

KU KARANTA : Matar Sadiq Sani ta haifi Budurwa

Dan autan sayayyan Man Utd Lukaku zai gurfana a gaban Kotu

Man Utd ta saye Dan wasa Romelu Lukaku

Da farko sai da 'Yan doka su ka gargadi Dan wasan da sauran mutanen da ke cashewar kusan sau 6 amma duk da haka ba su tsagaita ba. Daga baya dai Jami'an tsaro su ka kama Dan wasan kuma zai bayyana gaban Kotu zuwa watan Oktoba.

Manchester United ta sayo Dan wasa Romelu Lukaku daga Everton kan kudi kusan Miliyan £75 wanda ana tsammani ya karu nan gaba. Shi kuma Dan wasa Rooney ya koma Kungiyar da ya baro tun yana Dan shekara 18 watau Everton.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ka ji abin da Ronaldo yayi wa Davido

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel