Madalla! Za'a fara aikin samar da 200MW ta wutar lantarki daga rana a Arewa

Madalla! Za'a fara aikin samar da 200MW ta wutar lantarki daga rana a Arewa

- Gwamnan Kano ya sa hannu a yarjejeniyar samar da wutar lantaki

- Kamfanoni biyu ne dai za su yi aikin

- Gwamna Ganduje na aiki

Labarin da muka samu da dumi-dumin sa yana nuni da cewa zababben Gwamnan Kano Alhaji Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da masu mashahuran kamfanoni biyu da suka kware a harkar makamashi sun sanya hannu wa wata takardar yarjejeniya.

Ita dai wannan yarjejeniya kamar yadda majiyar mu ta ruwaito na da nufin samar wa jihar Kano da wutar lantarki daga hasken rana mai yawan gaske ta takai mega wat 200 watau 200MW.

Madalla! Za'a fara aikin samar da 200MW ta wutar lantarki daga rana a Arewa

Madalla! Za'a fara aikin samar da 200MW ta wutar lantarki daga rana a Arewa

NAIJ.com ta samu labarin cewa kamfunan dai sune Blacrhino da kuma kamfanin Dangote sune wadanda zasu gudanar da aiki, ana sa ran zasu kammala dukkan ayyukan cikin wata goma sha takwas In sha Allah.

A baya ma dai gwamnatin ta jihar Kano ta fara shirin yadda za'ayi ta fara samar da wutar lantarkin daga bola.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel