Cakwakiya a cikin gidan PDP: Ali Modu ya sake samun rinjaye akan Makarfi

Cakwakiya a cikin gidan PDP: Ali Modu ya sake samun rinjaye akan Makarfi

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben cike gurbi na sanatan mazabar Osun ta kudu, Cif Jackson Adeleke ya samu nasarar lashe zaben kujerar daya gudana a ranar asabar 8 ga watan Yuli.

Sai dai nasarar da Cif Adeleke ya samu ta sake motsa adawa da ja-in-ja dake tsakanin bangarorin dake ikirarin shugabancin jam’iyyar ta PDP, wato bangaren Ali Modu Sheriff dana Ahmed Makarfi.

KU KARANTA: Iyaye su dage wajen sanya ýaýansu haddar Al-Qur’ani – Sarkin Musulmi

NAIJ.com ta ruwaito PDP bangaren Sanata Sheriff suna taya dan takarar murna, inda suka ce sune suka bashi tutar tsayawa takara, kuma a wajen su ya siya takardar cikewa domin zaman dan takarar, sa’annan su suka bashi tikitin tsayawa takara.

Cakwakiya a cikin gidan PDP: Ali Modu ya sake samun rinjaye akan Makarfi

Sheriff yayin daya baiwa Adeleke tuta

Yayin da Sheriff ke wannan batu, shi kuwa, Sanata Makarfi kira yake yaji dadi dan takarar jam’iyyar su ta PDP ya lashe zaben kujerar sanatan Osun ta kudu, inda yace duk wani dan halaliyar PDP, toh a karkashin shugabancinsa yake.

Cakwakiya a cikin gidan PDP: Ali Modu ya sake samun rinjaye akan Makarfi

Adeleke yayin da ya kawo gaisuwa PDP

Wannan zabe dai ya biyo bayan rasuwar tsohon Sanata Isiaka Adeleke, wanda yake yaya ne ga Jackson Adeleke wanda ya samu nasara a zaben ranar Asabar, inda ya lashe kashi 61.35 na kuri’un yayin da APC ke da kashi 31.11.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

APC ba jam'iyya bace, inji wani mutum, Kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel