Tsugune bata kare ba! Hukumar EFCC ta shirya tsaf don sake gurfanar da Sule Lamido kotu

Tsugune bata kare ba! Hukumar EFCC ta shirya tsaf don sake gurfanar da Sule Lamido kotu

- Tsugune bata kare wa tsohon Gwamnan Jigawa ba

- EFCC tace ta shirya tsaf domin kara gurfanar da shi

- A baya dai an bada belin sa

Labarin da muke samu yanzu na nuni da cewa hukumar dake da alhakin yaki da cin hanci da rashawa ta kasa watau EFCC a takaice ta ce ta shirya tsaf domin sake gurfanar da Alhaji Sule Lamido kotu.

Shidai Sule Lamido gawurtaccen dan siyasa ne kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP. Haka zalika ma dai shine tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke da iyaka da Bauchi, Kano da kuma Katsina.

Tsugune bata kare ba! Hukumar EFCC ta shirya tsaf don sake gurfanar da Sule Lamido kotu

Tsugune bata kare ba! Hukumar EFCC ta shirya tsaf don sake gurfanar da Sule Lamido kotu

NAIJ.com dai ta tuna cewa a kwanan baya dai hukumar ta EFCC ta gurfanar da Sule Lamido din da yayan sa biyu Aminu da Mustapha a gaban wata babbar kotu inda kuma aka zarge su da aiwatar da laifuka kusan 43 ciki hadda almubazaranci da kuma baba kere da dukiyar jama'a.

Sai dai wadan da ake zargin ko kusa basu amince da tuhume-tuhumen da ake yi masu ba inda kuma a baya din aka bayar da belin su.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel