Shugaban Amurka ya karɓi bakoncin ýan matan Chibok a fadar White House (HOTUNA)

Shugaban Amurka ya karɓi bakoncin ýan matan Chibok a fadar White House (HOTUNA)

- Wasu yan matan Chibok sun jinjina ma shugaban kasar Amurka Donald Trump

- Wadannan yan matan Chibok sun gabatar da wanta wasika ga Trump

Wasu yan matan Chibok Joy Bishara da Lydia Pogu sun jinjina ma shugaban kasar Amurka Donal Trump ta cikin wata wasika da suka karanta masa a gabansa yayin daya karbi bakoncinsu a ofishinsa.

Wadannan yan matan Chibok su biyu sun gabatar da wannan wasika ne yayin da suka kai ma Trump ziyara a fadar shugaban kasar Amurka dake White House, inda suka bashi labarin halin da suka shiga a baya yayin da suke hannun Boko Haram.

KU KARANTA: Shirye shiryen 2019? Atiku ya halarci taron jam’iyya mai mulki ta ƙasar Ingila (HOTUNA)

NAIJ.com ta gano yan matan na daga cikin wadanda suka tsere daga hannun mayakan Boko Haram a lokacin da suka sace su a shekarar 2014 daga makarantarsu yayind a suke zana jarabawa.

Shugaban Amurka ya karɓi bakoncin ýan matan Chibok a fadar White House (HOTUNA)

Trump yana sauraran yan matan

“Ya shugaba, muna bukatar da ka karfafa tsaro a Amurka, mun san wasu mutane na kokarin su kawra maka da hankali, kada ka yarda. Idan Amurka bata kasance karfaffa a duniya ba, a ina zamu sauki idan mun shiga halin ni yasu?” inji wasikar da suka karanta ma Trump.

Shugaban Amurka ya karɓi bakoncin ýan matan Chibok a fadar White House (HOTUNA)

Yarinyar Trump tare da ýan matan Chibok

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito yan matan sun kammala karatunsu a wata jami’a a kasar Amurka, kuma sun samu rakiyar shugaban makarantar, Doug Wead.

Ga sauran hotunan:

Shugaban Amurka ya karɓi bakoncin ýan matan Chibok a fadar White House (HOTUNA)

Trump da yan matan

Shugaban Amurka ya karɓi bakoncin ýan matan Chibok a fadar White House (HOTUNA)

Diyar Trump da yan matan Chibok

Shugaban Amurka ya karɓi bakoncin ýan matan Chibok a fadar White House (HOTUNA)

Diyar Trump da yan matan

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani minista ya dace Buhari ya sallama?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel